Cardiff City ta kori Mackay

Image caption Malky Mackay ne ya mayar da Cardiff Premier bayan fashin shekaru 52.

Cardiff City ta kori kocinta Malky Mackay bayan wani taro da hukumar daraktocin kungiyar ta yi.

Sanarwar da kungiyar ta fitar a shafinta na intanet ta ce za'a nada sabon koci nan ba da jimawa ba.

Shekaru biyu da rabi Mackay ya yi Cardiff, inda ya mayar da kungiyar rukunin Premier bayan fashin shekaru 52.

Korar ta sa na zuwa ne kasa da sa'o'i 24 bayan da kungiyar ta sha kaye 3-0 a hannun Southampton a gasar Premier.

Ta kuma biyu bayan sabanin da aka samu tsakanin mamallakin kungiyar Vincent Tan da kocin.