Arsenal na ci gaba da haskakawa

Image caption Kocin Arsenal, Arsene Wenger

Arsenal za ta kamalla shekara ta 2012 a matsayin ta farko a kan teburin gasar Premier ta Ingila saboda doke Newcastle da ci daya me ban haushi a ranar Lahadi.

Olivier Giroud ne yaci kwallon, abinda yasa suka shiga gaban Manchester City a saman teburin gasar.

A yanzu Chelsea ce ta uku, Everton ta hudu sai kuma Liverpool ta biyar.

Wasannin Premier a ranar 1 ga watan Junairu:

*Swansea v Man City*Arsenal v Cardiff*Crystal Palace v Norwich*Fulham v West Ham*Liverpool v Hull*Southampton v Chelsea*Stoke v Everton*Sunderland v Aston Villa*West Brom v Newcastle*Man Utd v Tottenham

Karin bayani