Ba zamu sayar da Balotelli ba - AC Milan

Image caption Mario Balotelli da Robinho da kuma De Jong na murna

Kungiyar AC Milan ta karyata rahotannin dake cewar dan kwallonta Mario Balotelli zai bar kungiyar a watan Junairu.

Sun maida martani ne a kan rahotanni cewar shugaban AC Milan Silvio Berlusconi na shirin sayar da dan kwallon.

Tsohon dan kwallon Manchester City din mai shekaru 23 ya zura kwallaye shida wasanni 12 a gasar Serie A ta bana.

Balotelli ya koma San Siro ne a watan Junairun bana a kan fan miliyan 19.

A kakar wasan da ta wuce ya zura kwallaye 12 a Milan cikin wasanni 13.

Karin bayani