Everton ba za ta sayar da Barkley ba

Image caption Ross Barkley na haskakawa

Kocin Everton Roberto Martinez ya ce kungiyar ta na cikin yanayin da ya dace a fannin kudi, da zai hanata sayar da Ross Barkley a watan Junairu.

Barkley mai shekaru 20 ana alakantashi da komawa Manchester United a kan fan miliyan 50.

Barkley ya haskaka a kakar wasa ta bana a Everton inda ya zura kwallaye uku sannan kuma Ingila ta gayyaci shi sau uku don ya taka mata leda.

Tsohon kocin Everton David Moyes wanda ya koma United, tuni ya raba tsohuwar kungiyarsa da Marouane Fellaini sannan kuma yake ta zawarcin Leighton Baines.

Karin bayani