Bendtner zai yi jinyar makwanni

Nicklas Bendtner
Image caption Arsenal za ta yi karacin masu zura kwallo a raga

Dan kwallon Arsenal Nicklas Bendtner zai yi jinyar rauni a idon sawunsa na tsawon makwanni, hakan zai sa kungiyar ta yi karancin 'yan wasa masu zura kwallo a raga.

Dan wasan Denmark shine ya fara zura kwallo a ragar Cardiff a wasan da suka lashe da ci biyu da nema, a wasan da ya shigo sauyi ya kuma ji rauni a kafarsa.

Shi kuwa dan wasan Arsenal, Olivier Giroud bai samu damar buga wasan ba sakamakon rauni da yake da shi a kafarsa.

Da yake an bude kasuwar sayen 'yan wasa, kocin kungiyar Arsene Wenger ya tabbatar da cewar kungiyar na karancin 'yan wasa masu zura kwallo a raga.

Sai dai bashi da tabbacin ko hakan zai sa ya shiga kasuwar sayen 'yan wasa masu zura kwallo a cikin watan Janairun nan.

Kungiyar bata da tabbacin ko Bendtner zai samu buga mata gasar kofin kalubale da za su kara da Tottenham, wanda shima Giroud ba tabbas.

Haka suma 'yan wasa Aaron Ramsey da Mesut Ozil da Kieran Gibbs da Tomas Rosicky ba za su sami buga karawar da Arsenal za tayi da Cardiff ba sakamakon jinyar rauni.