Lampard da Ivanovic za su yi jinya

Image caption Magoya bayan Chelsea na fata kada jinyar ta yi tsawo

'Yan kwallon Chelsea Frank Lampard da Branislav Ivanovic za su yi jinyar wata guda saboda rauni.

Kocin Chelsea Jose Mourinho, ya bayyana cewar an sun samu rauni ne a wasansu da Liverpool da suka samu nasara daci biyu da daya.

Ivanovic mai shekaru 29, ya samu rauni a gwiwarsa a wasansu na ranar 29 ga watan Disamba.

Shi kuma Lampard ya ji rauni ne a kafarsa.

Lampard mai shekaru 35, ya zura kwallaye hudu a wasanni 18 da ya bugawa Chelsea a kakar wasa ta bana.

Shi kuwa Ivanovic dan kasar Serbia ya bugawa Chelsea wasanni 26 kawo yanzu.

Karin bayani