Moyes ya caccaki alkalin wasa

Image caption David Moyes

David Moyes ya ce abin 'kunya' ne da aka hana Manchester United bugun fenariti a wasan da suka sha kashi a hannun Tottenham a Old Trafford a gasar Premier.

United ta sha kashi daci biyu da daya, amma kuma golan Spurs Hugo Lloris, ya kayar da Ashley Young a cikin gidan Spurs din, amma alkalin wasa yaki bada fenariti.

Moyes yace "Hukuncin bai dace ba, kuma shine mafi muni da zan iya tunawa".

Sannan kuma ya caccaki Howard Webb saboda baiwa Adnan Januzaj katin gargadi saboda lambo.

Shi ma kocin Tottenham, Tim Sherwood ya ce ya dauka za a bada bugun fenariti.

Karin bayani