Reuben sun raba gari da Kilmarnock

Gabriel Reuben
Image caption Dan wasan ya yi murna da zai bar kungiyar

Dan kwallon Nijeriya Gabriel Reuben sun raba gari da kulob dinsa Kilmarnock ta Scotland bayan da kungiyar ta amince da soke yarjejeniyar da suka kulla.

Rueben, mai shekaru 23 wanda tsohon dan kwallon Kano Pillars ne, ya sanya hannu a kwangilar shekaru uku a watan Afrilun bara.

Dan wasan bai samu damar buga wasanni ba a-kai -a-kai sakamakon jinyar rauni da ya yi fama da ita, a watan Nuwamba ya nemi kulob din da ya soke yarjejeniyar da suka kulla, domin ya bar kungiyar.

Reuben ya sami sauki a watan Augusta, bayan da ya kwashe watanni uku yana jinya, kuma yana cikin 'yan wasan Nijeriya da suka sama mata tikitin shiga kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci a bana.

Dan wasan ya yanke hukuncin barin Kilmarnock ganin baya buga wasa, da zummar sauya sheka ko zai sami damar wakiltar Nijeriya a gasar Kofin duniya a badi.