FA: Arsenal za ta kara da Coventry

FA Cup Fouth Routh
Image caption Arsenal na fatan lashe kofi a bana

Arsenal za ta karbi bakuncin Coventry City a filin ta na Emirates, a wasan zagaye na hudu a gasar kofin kalu-bale wato FA Cup.

Rabon da Arsenal ta dauki kofin FA tun a shekarar 2005, kuma Blackburn Robers ce ta fidda Arsenal a zagaye na biyar a shekarar bara.

Chelsea za ta kara da Stoke City a Stamford Bridge, a inda Manchester City za ta fafata da Bristol City ko Watford, idan City ta samu nasara a wasan da za su sake karawa da Blackburn, bayan da suka tashi a wasan farko 1-1.

Za a fara gumurzu a wasannin Fa ranar 25 da 26 ga watan Janairu.

Duk kungiyar da ta samu nasara a karawa tsakani Manchester United da Swansea, za ta fafata da Birmingham City ko Bristol Rovers ko Crawley.

Zakara mai rike da kofi Wigan, za ta karbi bakuncin Crystal Palace, idan ta lashe MK Dons a wasa na biyu da za su sake barje gumi, bayan da suka tashi wasan farko 3-3 a karawar da suka yi ranar Asabar.

Everton za ta ziyarci Stevenage, Cardiff da Bolton Wanderers, sai Liverpool ta kara da Bournemouth ko Burton, idan ta lashe Oldham.