FA: Swansea ta yi waje da United

FA Swansea win United
Image caption An cire United a kofin kalu bale wato FA na bana

Swansea City tayi waje da kungiyar Manchester United har gida a gasar kofin kalu-bale da ci 2-1 a wasan zagaye na uku.

Nasarar da Swansea ta samu a Old Trafford, itace ta farko a tsawon shekaru hudu da suka gabata.

Wayne Routledge shine ya fara zura kwallo da kai a ragar United, daga baya Javier Hernandez ya farke kwallo daga bugun da Alex Buttner ya bugo kwallo, kuma wasa ya koma 1-1.

Dan wasan United Fabio da ya shigo canjin Ferdinand lokacin da ya ji rauni, an bashi jan kati sakamakon keta da yayi wa Jose Canas, daga baya daf a tashi wasa Wilfried Bony ya zurawa United kwallo ta biyu a raga.

Da yake an cire United a gasar bana, Swansea za ta kara da Birmingham ko Bristol Rovers ko Crawley a wasan zagaye na hudu.