Blatter ya koka da shirin Brazil 2014

Image caption Ana samun jinkiri a shirin gasar Brazil 2014.

Shugaban hukumar Fifa, Sepp Blatter ya soki Brazil kan jinkirin shirin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya.

Sepp Blatter ya ce: "Babu wata kasa da ta taba samun irin jinkirin da Brazil ta samu tun farkon zuwa na Fifa."

"Wannan ce kasar da ta fi kowacce a baya samun tsawon lokacin da za ta shirya wa karbar bakun gasar."

Shekaru bakwai da suka gabata ne aka tabbatar wa da Brazil damar daukar nauyin gasar da za'a gudanar a bana sai dai kawo yanzu shirye-shirye ba su kammala ba.