FA ta wanke Clattenburg daga zargi

Mark Clattenburg
Image caption FA bata samu alkalin wasan da laifi ba

Hukumar kwallon kafar Ingila ta wanke alkalin wasa Mark Clattenburg daga zargin da kungiyar Southampton ta shigar a kansa.

Kaftin din Saints, Adam Lallana ya kalubalanci Clattenburg bayan da alkalin wasa yaki bada bugun fenariti har sau biyu kamar yadda suka zarga a wasan da suka yi rashin nasara a hannun Everton.

An ce alkalin wasan ya ce da Lallana. "Bamu sanka da wannan halin ba, amma ka canja bayan da ka bugawa Ingila wasa."

Hukumar gudanar da Premier taki karbar korafin da kungiyar ta shigar a makon da ya gabata.