Jordan Ayew ya koma Sochaux

Image caption Jordan da yayansa Andre Ayew

Dan wasan tsakiyar Ghana, Jordan Ayew zai kammala kakar wasa ta bana a Sochaux bayan da Marseille ta ba da aronsa ranar Litinin.

A makon jiya ne kungiyoyin biyu da ke bugu rukunin Ligue 1 na Faransa suka amince da hakan.

Ayew mai shekaru 22 ya buga wa Marseille wasanni 111 inda ya zura kwallaye 14 tun farkon daukarsa a 2009.

Dan wasan ya taka rawar gani wurin sama wa Ghana gurbi a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a Brazil.