Ferdinand zai yi jinyar makwanni biyu

Rio Ferdinan
Image caption Ya shiga jerin 'yan wasan kungiyar masu jinyar rauni

Dan wasan Manchester United Rio Ferdinand zai yi jinyar sati biyu a raunin da ya ji a gwiwarsa.

Tsohon dan kwallon Ingila mai tsaron baya, mai shekaru 35 ya samu raunin ne a karawar da Swansea ta lashe United ranar Lahadi a gasar kofin kalu-bale.

Raunin da dan wasan ya ji ba mai tsauri bane, domin kujewa ya yi, kuma babu karaya ko gocewar kashi kamar yadda aka yi tsammani tun a farko.

Dan wasan ba zai samu bugawa United wasanni uku ba, sai dai zai buga karawar da kungiyar za ta karbi bakuncin Sunderland a wasan kusa dana karshe a kofin Capital One.

Tuni United ke fama da 'yan wasa masu jinyar rauni da suka hada da Robin van Persie da Wayne Rooney da Ashley Young da Marouane Fellaini da kuma Phil Jones.