FIFA ba ta tsayar da magana kan Qatar ba

Image caption Filin wasa na Alshamal na Qatar

Hukumar dake kula da kwallon kafa a duniya wato FIFA ta ce ba a tsayar da magana ba a kan lokacin da za a gudanar da gasar cin kofin duniya shekara ta 2022 da aka shirya yi a Qatar.

FIFA ta bayyana cewar babu hukuncin da aka dauki kan batun har sai bayan kamalla gasar cin kofin duniya na bana da Brazil za ta dauki bakunci.

Matakin na FIFA ya biyo bayan kalaman sakatare janar din ta wanda yace gasar cin kofin kwallon kafa na shekara ta 2022 da aka shirya yi a Qatar, ba za ta gudana a watannin da aka saba yi wato Yuni da Yuli.

Jerome Valcke ya ce zai fi kyau a yi gasar daga tsakiyar watan Nuwamba locakin da babu matsanancin zafi a Qatar.

Tsananin zafin da ake yi a Qatar a watannin Yuni da Yuli ne ya sa hukumar FIFA dage lokacin da aka saba gudanar da gasar.

Karin bayani