A Barcelona zan yi ritaya — Messi

Lionel Messi
Image caption Dan wasan ya zura kwallaye biyu a ragar Getafe

Dan kwallon Barcelona, Lionel Messi, ya ce yana fatan karasa wasanninsa har lokacin da zai yi ritaya a Barcelona.

Kyaftin din Argentina ya zura kwallaye biyu, bayan da ya dawo daga jinyar raunin da ya yi ranar Laraba, a wasan da Barcelona ta casa Getafe da ci 4-0 a gasar kofin Copa del Rey.

Messi ya ce, "Ina son yin ritaya a Barcelona tunda magoya bayan kulob din na kaunata, kuma daga kungiyar ba na fatan bugawa wata kungiyar wasa."

An dade ana tantamar makomar dan wasan a Barca tun lokacin da suka samu rashin jituwa da Dirakta Javier Faus akan tsawaita kwangilarsa da kungiyar.

An ruwaito Faus yana dagewa cewa ba wajibi ba ne su sabunta kwantaragin Messi, wacce za ta kare a cikin watan Fabrairu zuwa Yuni shekarar 2018.

Messi, mai shekaru 26, ya zargi Faus a Disamba da cewa bai san komai ba akan kwallon kafa.

Dan wasan zakaran kwallon duniya karo hudu ya yi fama da jinya a bara, kuma raunin da ya yi a baya bayan nan shi ne wanda ya ji a wasan da Barca ta doke Real Betis da ci 4-1 a watanni biyu da suka wuce.