Smalling ya tuba da "kunar-bakin-wake"

Image caption Chris Smalling ya ce shigar ba ta dace ba.

Dan wasan Manchester United Chris Smalling ya nemi afuwa bayan da hotonsa ya bayyana sanye da shigar 'yan kunar bakin wake a wajen wata liyafar bad da kama.

Jaridar the Sun ta Britaniya ta ranar Alhamis ta wallafa hoton dan wasan na Ingila sanye da rawani da rigar 'yan kunar bakin wake, da jigidar kwalaben barasa a maimakon bama-bamai.

Sanarwar da wakilan dan wasan su ka bayar ta ce sanya wanann tufafin kuskure ne kuma bai dace ba.

Sun kuma ce Smalling na neman gafarar duk wanda hoton ya bata musu rai.