Mel Pepe ya zama kocin West Brom

Image caption Pepe Mel ne ya mayar da Real Betis La Liga bayan ta fada Segunda Division.

West Brom ta nada tsohon kocin Real Betis, Pepe Mel a matsayin kocinta na tsawon watanni 18.

Kungiyar da ke buga wa wasa a Premier ta shiga neman koci ne bayan korar kocinta Steve Clarke ranar 14 ga Disamba.

West Brom ta fara tuntubar Mel dan Spain mai shekaru 50 ne a Disamba amma sai maganar ta shiriri ce bayan da ya bayyana aniyarsa ta tahowa da tawagar mataimakansa.

Yanzu dai an amince zai yi aikin ne tare da mataimakin kocin West Brom Keith Downing da kocin masu tsaron gida Dean Kiely.

Mel, wanda tsohon dan wasan gaba ne a Betis ya zamo kocin kungiyar a 2010 inda ya jagorance ta zuwa koma wa La Liga bayan da ta zama zakarar rukunin Segunda Division cikin shekara guda.