Juve ta tsawaita lashe wasanni 11 a jere

Juventus
Image caption Kungiyar tana taka rawar gani a bana

Kungiyar Juventus ta tsawaita lashe wasannin 11 a Seria A na Italiya, bayan da ta doke Cagliari da ci 4-1 a wasan sati na 19.

Cagliari ce ta fara zura kwallo ta hannun dan wasanta Mauricio Pinilla amma daga baya aka bashi jan kati ya kuma futa daga wasan.

Fernando Llorente shi ne ya farkewa Juve kwallo da kuma zura kwallo ta uku a raga, Claudio Marchisio da aka sauya a wasan shine ya zura kwallo ta biyu, kafin daga baya Stephan Lichtsteiner ya zura kwallo ta hudu a raga.

Nasarar da Juve ta samu ta baiwa Roma tazarar maki takwas da kuma ci gaba da zama ta daya a teburin Seria A, a kokarin da take na lashe kofin bana.

Juventus ta taba lashe wasanni 10 a jere a karshen kakar wasanni ta 1931-32