Manchester City ta doke Newcastle 2-0

Manchester City
Image caption City ta dare matsayi na daya kafin Arsenal ta yi wasa

Manchester City ta dare matsayi na daya a teburin Premier bayan da ta doke Newcastle da ci 2-0 har gida a karawar wasan sati na 21.

City ce ta fara zura kwallo ta hannun dan wasanta Edin Dzeko a minti na takwas da fara kwallo, Newcastle ta farke kwallo ta hannun Cheick Tiote amma alkalin wasa Michael Jones ya ki karbar kwallon ya ce anyi satar gida.

Sau biyu Yohan Cabaye dan kwallon Newcastle ya kusan zura kwallo a raga, kafin City ta zura kwallo ta biyu ta hannun dan kwallonta Alvaro Negredo.

Manchester City tana matsayi na daya a teburin Premier da maki 47, sai Chelsea a matsayi na biyu da maki 46, bayan da suka buga wasanni 21.

Aston Villa za ta karbi bakuncin Arsenal a filin wasa na Villa Park ranar Litinin a gasar Premier wasan sati na 21.