Mba na fatan buga kofin duniya

Sunday Mba
Image caption Dan wasan yana fatan buga gasar kofin duniya a Brazil

Dan kwallon Najeriya Sunday Mba na shirin kara kaimi a wasanninsa domin buga gasar kofin duniya, bayan da ya yi wasan farko a sabuyar kungiyar da ya koma CA Bastia ta Faransa.

Dan wasan mai shekaru 25, wanda ya zura kwallon da ya baiwa Nageriya damar lashe kofin Afirka a Fabrairun bara, sai a bana ne ya samu kungiya a Turai da yake buga wa wasa.

Kungiyoyi da dama sun sha tattaunawa akan daukar tsohon dan kwallon Warri Wolves, kuma kusan kimanin shekara guda kenan tun bayan kammala gasar kofin Afirka.

A ranar Juma'a ne dai sabuwar kungiyar da ya koma ta sha kashi a hannun Niort da ci 3-0 a gasar Faransa ta 'yan rukuni na biyu.