AC Milan ta kori Massimiliano Allegri

Massimiliano Allegri
Image caption Milan na fama da koma baya a kakar wasan bana

Kungiyar AC Milan ta raba gari da kocinta Massimiliano Allegri, kwana daya bayan da kungiyar ta yi rashin nasara da ci 4-3 a hannun sabbin shiga gasar Serie A Sassuolo.

Rashin nasarar da kungiyar ta yi yasa ta koma matsayi na 11 a teburin Seria A, da tazarar maki 30 tsakaninta da Juventus wacce take matsayi na daya a teburi.

Allegri, mai shekaru 46, wanda kwangilarsa da kungiyar za ta kare a karshen kakar wasan bana, yanzu ya bar kungiyar tare da masu taimaka masa.

Kungiyar ta nada tsohon dan wasanta kuma mataimakin koci Mauro Tassotti, a matsayin kocin riko.

Allegri, tsohon kocin Cagliari ya jagoranci Milan a inda ta lashe kofin Seria A, a shekarar farko da ya maye gurbin Leonardo a watan Yunin 2010.