Ronaldo ya zama dan kwallon duniya

Image caption Dan kwallon duniya 2013

Dan wasan Portugal da Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya lashe gasar gwarzon kwallon duniya ta ballon d'Or ta 2013.

Hukumar kwallon kafa ta duniya ce ta tabbatar masa da wannan kyauta da yammacin Litinin a Zurich, Switzerland.

Kyaftin din na Portugal mai shekaru 28 ya doke Lionel Messi ne na Argentina da Barcelona da Frank Ribery na Faransa da Bayern Munich.

Ronaldo ya zura kwallaye 66 a raga cikin wasanni 56 da ya buga wa kasarsa da kungiyarsa.

Wannan ne karo na biyu da Ronaldo ya samu kyautar bayan da ya taba lashe ta a 2008.

Karin bayani