Liverpool ta casa Stoke 5-3

Image caption Luis Suarez ya zura kwallaye biyu a wasan.

Sau biyu Luis Suarez ya na zura kwallo a wasan da Liverpool ta samu nasararta ta farko kan Stoke City a rukunin Premier, inda ta rage tazarar da ke tsakaninta da jagorar rukunin Manchester City zuwa biyar.

Kafin rabin lokaci Liverpool na gaba da 2-0 bayan da Ryan Shawcross na Stoke ya ci gida sannan Suarez ya zura guda.

Peter Crouch ne ya zare daya da ka sannan Charlie Adam ya mai da wasan 2-2.

Kwallayen Steven Gerrard, Luis Suarez da Daniel Sturridge ne suka tabbatar da nasarar Liverpool.