Fifa za ta sauya dokokin kwallon kafa

Image caption Shugaban Fifa, Sepp Blatter

Hukumar Fifa za ta saurari shawarwari game da sauya dokokin hukunta 'yan wasan kwallon kafa.

A watan jiya ne dai shugaban Uefa Michel Platini ya nemi a sauya katin gargadi da dakatar da dan wasa tsawon mintuna 10 zuwa 15.

Fifa ta kafa kwamitoci biyu, inda dayansu ya kunshi tsofaffin 'yan wasa da masu horarwa dayan kuma ya kunshi mahukunta da kwararru kan kwallon kafa domin tattauna batun.

Kwamitocin za su gabatar da rahotonsu ne gaban majalisar kwallon kafa ta duniya, IFAB - wacce ta kunshi FIFA da hukumomin kwallayen kafa na Brtaniya - wacce ke da alhakin sauya dokokin kwallon kafa a duniya.