Pardew ya nemi afuwar Pellegrini

Image caption Pardew na zargin rafali bai wa Newcastle adalci ba.

Kocin Newcastle, Alan Pardew ya ce bai fahimci dalilin da ya sa rafali ya hana kwallon da Cheick Tiote ya zura a ragar Manchester City ba, amma ya nemi afuwar martanin da ya mai da.

Rafali, Mike Jones bai ba da kwallon da Tiote ya zura ba a wasan da Manchester City ta yi nasara 2-0.

Pardew ya baiyana nadamar zagin da ya yi wa Manuel Pellegrini na City yayin da aka tafi hutun rabin lokaci.

Ya ce; "A fusace na ke a lokacin."

Sai dai bayan wasan Pellegrini ya ce Pardew "ya yi ta korafi kan duk hukuncin da rafali ya dauka."