Gutierrez ya koma Norwich City

Image caption Jonas Gutierrez

Norwich City ta karbi aron dan wasan Newcastle united Jonas Gutierrez zuwa 30 ga Yuni.

Dan Argentinan mai shekaru 30 ya rubuta a Twitter ranar Laraba cewa nan take zai bar filin St James Park.

Gutierrez ya taka muhimmiyar rawa a kungiyar Magpies lokacin da Chris Hughton ya jagorance su zuwa Premier daga rukunin Championship a shekarar 2010.

Gutierrez, wanda sau biyu tak ya buga wa Newcastle wasa a kakar bana, ya ce: "Ina farin cikin kasancewa a nan domin dama ce ta komawa wasa."