Za mu iya lashe Premier - Wenger

Image caption Kocin Arsenal, Arsene Wenger

Arsene Wenger ya gargadi kungiyoyin da ke kasayya da Arsenal wurin daga kofin Premier a bana cewa kungiyarsa na da damar lashe kofin bayan da ta sake koma wa sama da nasarar da ta samu a Aston Villa.

Jack Wilshere da Olivier Giroud ne suka fara bai wa Arsenal zarra a rabin lokacin farko amma Christian Benteke ya zare wa Villa kwallo daya bayan dawowa daga hutu.

Kocin na Gunners, Arsene Wenger ya ce: "Kowa ya sa mana ido ya ga ko za mu sauka daga matsayinmu bayan da sauran kungiyoyin su ka yi nasara."

Ya kara da cewa; "Martanin da za ka iya mayar wa shi ne ka yi nasara; kuma mun yi."