Arsenal ta koma matsayinta a Premier

Arsenal Villa
Image caption Arsenal tana taka rawar gani a gasar wasanni ta bana

Arsenal ta dare matsayi na daya a teburin Premier bayan da ta doke Aston Villa da ci 2-1 har gida a gasar Premier wasan sati na 21.

Gunners ce ta fara zura kwallaye biyu ta hannun 'yan wasanta Jack Wilshere da Olivier Giroud kafin Villa ta zare kwallo daya ta hannun Christian Benteke wanda rabonsa da jefa kwallo tun 14 ga watan Satumba.

Doke Villa da Gunners ta yi ya sa ta lashe wasanni 15 a jere, ta kuma dauki hanyar maimata yawan lashe wasa data kafa tarihi a Disambar 1998.

Wasan farko da suka kara a gidan Arsenal Villa ce ta lashe wasan da ci 3-1 a gaban 'yan kallon Arsenal.

Nasarar data samu yasa ta koma matsayinta na daya a teburi, Manchester City da Chelsea suka koma matsayi na biyu dana uku.

Arsenal za ta karbi bakuncin Fulham a fafatawar da za su yi a wasan sati na 22 ranar Asabar.