Gwarazan kwallon kafa na Fifa 2013

An sanar da gwarazan 'yan kwallon duniya 11 a bikin ba da kyautar Ballon d'Or ranar Litinin a Switzerland amma babu mai buga wasa a rukunin Premier a cikinsu.

Ga jerin 'yan wasan da suka kai bantensu:

Hakkin mallakar hoto Getty

MAI TSARON GIDA - MANUEL NEUR (Bayern Munich) Kowacce kungiya na bukatar mai tsaron gida na hakika, kuma wannan dan wasan na Jamus, mai shekaru 27 ya isa kwatance a Bayern Munich. Nutsuwar Neuer ta yi matukar rana a mamayar da kungiyarsa ta yi a gasar Bundesliga da Zakarun Turai.

Ko kun san? Ya yi wasanni 23 a 2013 a gasar Bundesliga da Zakarun Turai ba tare da an zura ko kwallo daya a ragarsa ba, abinda babu wani gola da ya iya yin haka cikin manyan rukunan kwallon kafa na Turai guda biyar.

DAN BAYA - DANI ALVES (Barcelona) Dan wasan Brazil Alves mai shekaru 30 dan baya ne gefen dama na gani na fada - wanda ke garzayawa gaba duk sanda dama ta samu, ba tare da sakaci da aikinsa na tsaro ba, abinda ya taimakawa Barcelona a 2013.

Ko kun san? Ya samar da damar zura kwallaye fiye da kowanne dan baya a La Liga a 2013, inda ya samar da damammaki 49.

Hakkin mallakar hoto CBF

DAN BAYA - THIAGO SILVA (Paris St-Germain) Akan ce 'yan bayan Brazil sun kware wurin rike kwallo, amma ba su iya kwatowa ba. Kyaftin din PSG mai shekaru 29 ya fatattaka wannan zance a shekarar da ya jagoranci kungiyarsa zuwa daukar kofin Faransa a karo na farko cikin shekaru 19 sannan ya daga kofin Confederation tare da Brazil.

Ko kun san? Thiago Silva ya yi nasarar yanka da kaso 72.9% a Ligue 1 a 2013, abinda ba wani dan wasan PSG da ya kusaci hakan. A wasannin tsawon mintuna 1736 da ya buga, sau tara kacal aka same shi da laifi.

Hakkin mallakar hoto AFP

DAN BAYA - SERGIO RAMOS (Real Madrid) Dan wasan na Spain na da saurin fushi abinda ke rage masa wasa a kungiyarsa ta Real Madrid saboda yawan jan katin da yake karba. Sai dai ba tantama a kwarewar dan wasan mai shekaru 27 wurin magance barazanar 'yan wasan gaba.

Ko kun san? Babu wani dan wasa da ya karbe kwallo daga abokan kasayya a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya na nahiyar Turai a 2013 fiye da Sergio Ramos, inda ya tare kwallaye 22.

Hakkin mallakar hoto Getty

DAN BAYA - PHILIPP LAHM (Bayern Munich) Kyaftin din Jamus da Bayern Munich mai shekaru 30 ya jagoranci kungiyarsa zuwa lashe gasar rukuni, kasa da duniya baki daya. Kuma zai jagoranci kasarsa a gasar cin kofin duniya a Brazil.

Ko kun san? Babu wani dan baya da ya bayar da kwallaye aka ci a manyan rukunonin kwallon kafa na Turai guda biyar a 2013 kamar Philip Lahm, wanda ya ba da kwallaye 10.

Hakkin mallakar hoto AP
Hakkin mallakar hoto Reuters

DAN TSAKIYA - XAVI (Barcelona) A matsayinsa na zuciyar Barcelona da Spain, Xavi mai shekaru 33 ne ke shiryawa kasarsa da kungiyarsa wasa ta hanyar kwarewar bada kwallo. Wannan ne karo na shida da Xavi ya shiga jerin kwararrun 'yan kwallon duniya.

Ko kun san? Kiyasin 2013 ya nuna cewa a kowanne wasan La Liga, Xavi ya yi nasarar bai wa 'yan kungiyarsa kwallo sau 83 - abinda ya zarta kowa a manyan rukunonin kwallon kafa guda biyar na Turai.

Hakkin mallakar hoto PA

DAN TSAKIYA - ANDRES INIESTA (Barcelona) Za'a ga bambarakwai idan Barcelona ta fita wasa ba tare da Iniesta mai shekaru 29 a gefen Xavi a tsakiyar fili ba. Dan gajeren dan wasan, wanda ya kwara wurin kai hari, ya shiga wannan jerin ne a karo na biyar a tarihi.

Ko kun san? Dan wasa daya ne tak ya yi nasarar mika kwallaye ga takwarorinsa fiye da Iniesta a gasar La Liga a 2013 inda ya mika kwallaye 2,303 wato kimanin kwallo 64 a kowanne wasa.

Hakkin mallakar hoto PA

DAN TSAKIYA - FRANCK RIBERY (Bayern Munich) Dan kwallon Faransa mai wasan gefe shi ne ruhin Bayern Munich a shekarar da ta lashe gasa a rukunin gida, Turai da duniya baki daya. Dan wasan mai shekaru 30 da ya shahara kan iya yanka da kuma cin kwallo, ya zamo gwarzon dan wasan nahiyar Turai na 2013.

Ko kun san? Ribery ya yi nasara a wasanni 41 cikin 45 din da ya buga wa Bayern a 2013 kuma ya fadi wasa daya ne tak. A wasanni 28 da ya buga wa Bayern Munich a Bundesliga kuwa, Ribery ya ci kwallo 12 kuma ya bayar an ci kwallaye 14.

Hakkin mallakar hoto Reuters

DAN GABA - CRISTIANO RONALDO (Real Madrid) Kyaftin din Portugal mai shekaru 28 ya ci kwallaye 66 a wasanni 56, ciki har da kwallaye ukun da ya ci wa kasarsa a nasarar da ta samu kan Sweden a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya. Sai dai bai samu nasarar taimakawa kungiyarsa Real Madrid ta ci kofi ko daya ba.

Ko kun san? Shi yafi kowanne dan wasa a manyan rukunonin kwallon kafa biyar na Turai zura kwallaye a 2013, inda ya ci kwallaye 38 a La Liga da 15 a gasar Zakarun Turai.

Hakkin mallakar hoto Reuters

DAN GABA - ZLATAN IBRAHIMOVIC (Paris St-Germain) Kyaftin din Sweden ne ya lashe kyautar kwallo mafi ban sha'awa ta Fifa a 2013. Dan wasan mai shekaru 32 ya nuna kwarewar murza zare inda ya taimakawa PSG ta daga kofin Faransa.

Ko kun san? Ibrahimovic ya ci kwallaye 27 ya bayar an ci 10 a wasa 36 a 2013, inda yafi kowa zura kwallaye a Ligue 1. Shi ne kuma yafi kowanne dan wasan kai hari raga, inda ya tamfatsa kwallaye 163 wanda 66 daga ciki suka isa bakin raga.

Hakkin mallakar hoto Getty

DAN GABA - LIONEL MESSI (Barcelona) Wannan ne karo na bakwai a jere da dan wasan gaban Argentina, Messi mai shekaru 26 ya shiga jerin gwarazan kwallon kafa na duniya. Kambun na Barcelona ya ci kwallaye 45 cikin wasanni 42, inda ya tallafawa kungiyarsa lashe gasar La Liga.

Ko kun san? A cikin kungiyoyi 17 da ya kara da su a La Liga, kungiya daya ce kurum, Atletico Madrid bai zura wa kwallo ba.