UEFA: Messi baya cikin 'yan kwallo 11

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya sha fama da jinya a karshen bara

Lionel Messi baya cikin kungiyar 'yan kwallon Turai 11 wato 'Uefa 2013', a makon da ya rasa kambunsa na gwarzon dan kwallon duniya wato ballon d'Or da Cristiano Ronaldo ya lashe.

Dan wasan Barcelona mai shekaru 26, ya kare a matsayi na 13 daga cikin mutane sama da miliyan shida da suka yi zaben ta shafin Uefa.

Shekaru bakwai kenan Cristiano Ronaldo ana zabensa a cikin 'yan kwallon Turai 11.

Dan kwallon Arsenal Mesut Ozil ne daga Premier da aka zaba, wanda a shekarar bara babu dan kwallon Premier ko daya.

Messi ya zura kwallaye 42 daga cikin wasanni 45 a shekarar bara da ya bugawa Argentina da Barcelona wasanni, amma ba a zabe shi ba, kuma babu wani dan kwallon Barcelona da aka zaba duk da kungiyar ta lashe La liga a 2013.

Rabon da ba a zabi Messi ba tun a shekarar 2007, amma yana cikin 'yan kwallon duniya 11 wato Fifpro da aka zaba ranar Litinin.

Ga wadanda jama'a suka zaba ta shafukan hukumar kwallon Turai da suka fi fice a bara

Mai tsaron raga: Manuel Neuer (Bayern Munich);

Masu tsaron baya: Sergio Ramos (Real Madrid), Thiago Silva (Paris St-Germain), Philipp Lahm (Bayern Munich), David Alaba (Bayern Munich)

Masu wasan tsakiya: Franck Ribery (Bayern Munich), Marco Reus (Borussia Dortmund) Mesut Ozil (Arsenal); Gareth Bale (Real Madrid),

Masu zura kwallo: Cristiano Ronaldo (Real Madrid), Zlatan Ibrahimovic (Paris St-Germain)