Matic na daf da komawa Chelsea

Nemanja Matic Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan ya bugawa Chelsea wasa shekaru uku baya

Nemanja Matic na daf da komawa tsohuwar kungiyarsa Chelsea akan kudi da zai kai fan miliyan 21.

Dan kwallon mai shekaru 25, wanda yake wasa a Benfica ta Portugal ya isa Landan domin duba lafiyarsa tun ranar Talata.

Matic na daf da komawa tsohuwar kungiyarsa da ya bari shekaru uku baya, kuma yana wasan tsakiya ne.

Dan kwallon Serbia ya bar Chelsea a shekarar 2011 kan kudi fan miliyan 5, lokacin da aka kimanta darajarsa har mai tsaron baya David Luiz ya dawo Chelsea daga Benfica.

Kocin Chelsea Jose Mourinho ne dai ya hangi gudun mawar da dan wasan zai bayar a kungiyar, ya kuma nemi ya dawo da shi, wanda tuni mahukuntan kungiyar suka amince da hakan.

Chelsea za ta biya kudin sayen dan wasan ne daga fan miliyan 16 da Wolfsburg za ta sayi Kevin De Bruyne daga kungiyar.