Baines zai tsawaita kwangilarsa da Everton

leighton baines Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karo biyu United ta nemi dan wasa a bara

Leighton Baines na gabda tsawaita kwangilarsa da kungiyar Everton domin ya ci gaba da buga mata kwallo.

Tsohon kocin Everton David Moyes sau biyu yayi kokarin dauko dan wasan mai shekaru 29 mai bugawa Ingila wasa domin ya bugawa Manchester United kwallo a kakar wasa ta bara.

Everton ta bada tabbacin cewa Baines, wanda aka sayo daga Wigan a Agustan 2007 zai rattaba hannun ci gaba da wasansa a kungiyar.

Ana kuma hangen kwangilar da Baines zai tsawaita, za ta kai kimanin fan 75,000 a kowanne mako.

A yanzu haka 'yan wasan Everton na hutu a Tenerife, kuma da zarar sun dawo daga hutu Baines zai rattaba sabuwar kwangila da kungiyar.

Everton kuma tana rarrashin Ross Barkley, mai shekaru 20, shima ya tsawaita kwangilarsa da kungiyar .