Man City na harin kofi hudu a bana

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Manuel Pellegrini na fatan kafa tarihi a Ingila.

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini ya ce ya na fatan daga kofunan gasa hudu da kungiyar ke bugawa a shekararsa ta farko.

City ce ta biyu a Premier, ta na jan West Ham da 6-0 a matakin kusa da na karshe na kofin Capital One sannan za ta kara da Barcelona a matakin 16 na karshe a gasar Zakarun Turai.

"Abin da wuya, amma za mu gwada" in ji Pellegrini da ya ke magana kafin wasa na biyu na zagaye na uku a gasar cin kofin kalubale da za su kara da Blackburn Rovers a gida.

Babu wata kungiya da ta taba daukar Premier, Zakarun Turai, Kalubale da League a kakar wasa daya.

Makwabciyar City Manchester United ta dau Premier, Kalubale da Zakarun Turai a kakar 1998-99 amma Tottenham ta fitar da ita a matakin daf da na kusa da na karshe na gasar kofin League.