Cole ya tsawaita kwangilarsa da West Ham

Carlton Cole Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya dawo kwallo da kafar dama

Dan kwallon West Ham Carlton Cole ya tsawaita kwangilarsa da kungiyar na tsawon watanni 18, bayan da ya shiga gajeriyar kwantaragi a watan Oktoba.

Cole, mai shekaru 30 ya kasa tabuka rawar gani a tsawon shekaru bakwai da ya yi a kungiyar.

Dan wasan ya dawo atisaye a watan Satumba ya kuma rattaba kwangilar watanni uku a watan Oktoba.

Ya zura kwallaye hudu a gasar Premier a wasanni 11 da ya buga, har da kwallaye uku da ya zura a wasanni shida baya.

QPR ta yi kokarin daukar tsohon dan kwallon Ingila, amma jinyar da Andy Carroll ya sha fama da ita ce ta kawo masu tsaiko.

Cole, ya koma West Ham ne daga Chelsea a shekarar 2006.