Seedorf ya zama kocin AC Milan

Clarence Seedorf Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Seedorf ya buga kwallo a kungiyoyi da dama a Turai

Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan dake Italiya ta dauki Clarence Seedorf a matsayin sabon kocinta.

Dan Holland din mai shekaru 37, ya bugawa Milan wasanni daga shekarun 2002 har zuwa 2012, ya kuma maye Massimiliano Allegri, bayan da kungiyar ta sallame shi sakamakon rashin tabuka rawar gani a kakar wasa bana.

Seedorf ya koma kwallo a Botafogo ta Brazil, ya kuma bada sanarwar daina buga kwallo bayan shekaru 22 da ya yi yana wasa, domin karbar aiki da tsohuwar kungiyarsa.

Tsohon dan kwallon Holland ya bugawa Milan sama da wasanni 400, ya kuma taimaka wa kungiyar lashe kofunan Seria A biyu da kofin zakarun Turai.

Haka kuma shi ne dan kwallon da ya fara lashe kofin zakarun Turai a kungiyoyi uku daban-daban-- ya dauka da Ajax a shekarar 1995 da Real Madrid a shekarar 1998 da Milan a shekarun 2003 da 2007.

Ya kuma buga wasa a kungiyar Inter Milan and Sampdoria.