Matic ya kara koma wa Chelsea

Nemanja Matic Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan ya koma kungiyar da ya bari a baya

Kungiyar Chelsea ta kammala sayen dan wasan Benfica mai wasan tsakiya Nemanja Matic bayan ya rattaba hannu a kwangilar shekaru biyar da rabi kan kudi fan miliyan 21.

Dan wasan mai shekaru 25 ya bar wasa a Stamford Bridge ya kuma koma Portugal a shekaru uku da suka wuce.

Chelsea za ta biya kudin dan kwallon da zarar ta karbi kudin cinikin dan wasanta Kevin De Bruyne da zai koma Wolfsburg ta Jamus.

Matic ya koma Chelsea ne dai daga kungiyar MFK Kosice ta Slovakia a shekarar 2009 kan kudi fan miliyan daya da rabi.

Dan wasan ya buga wasanni Premier biyu da ya shiga canji da kuma wasan da ya zauna canji lokacin da Chelsea ta doke Portsmouth da ci daya mai ban haushi a kofin FA wasan karshe a shekarar 2010.

Matic ya koma Vitesse Arnhem ta Holland aro a kakar wasa ta 2010 a watan Agusta, daga baya ya koma Portugal da akayi musaya Chelsea ta karbi mai tsaron baya David Luiz a Fabrairun 2011.

Banda Matic da Luiz, Chelsea ta taba daukar Ramires dan kwallon Brazil daga Benfika a shekarar 2010 kan kudi fan miliyan 17.