Hull na daf da daukar Long

shane long Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Saura kiris kwantaraginsa ta kare da West Brom

Kungiyar kwallon kafa ta Hull City na daf da daukar dan wasan West Brom mai zura kwallo a raga, bayan da kungiyoyin su ka amince akan kudi fan miliyan bakwai.

Long, mai shekaru 26 daf ya rage ya koma Tigers a ranar karshen cinikayyar 'yan kwallo a watan Satumba, amma za su sake tattaunawa ranar Alhamis.

Dan wasan Jamhuriyar Ireland, ya zura kwallaye 22 a wasanni 87 da ya bugawa West Brom, kuma sauran watanni 18 kwangilarsa ta kare da kungiyar.

Long ya zurawa kasarsa kwallaye 10 a wasanni 43, zai kuma bi sahun Nikica Jelavic tsohon dan kwallon Croatia da ya koma Hull kusan kudi daya.