Hukumar FA za ta ci tarar David Moyes

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Bakin Moyes ya ja masa hukunci

Kocin Manchester United David Moyes ya amince da tuhumar rashin ladabi da hukumar FA ta yi masa kuma ana sa ran cin sa tara.

Tuhumar dai ta shafi maganganun da ya yi ne bayan da Sunderland ta kada United 2-1 a wasan kusa da na karshe na gasar Capital One.

Moyes, mai shekaru 50 ya ce alkalan wasa ba sa yi wa Man U adalci a irin busar da suke yi mata.

Rafali Andre Marriner ya bai wa Sunderland fenariti wacce Fabio Borini ya yi amfani da ita ya ci kwallon da ta sa United faduwa a wasanni uku a jere a karo na farko tun Mayun 2002.

A baya dai an ci tarar kocin Liverpool, Brendan Rodgers £80,000 sanadiyyar maganganun da ya yi akan rafali a wasan da Manchester City ta doke kungiyarsa.

Karin bayani