FA za ta hukunta Anelka

Nicolas Anelka Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nunin da aka danganta da girmama 'yan nazi

A na sauraron hukuncin da hukumar kwallon kafar Ingila za ta yanke akan binciken data gudanar kan Nicolas Anelka bisa nuni da hannayensa da ya yi a makon jiya.

Dan wasan West Brom mai zura kwallo a raga ya yi nunin ne da aka fassara shi da jinjinawa 'yan Nazi, bayan da ya zura kwallo a ragar West Ham a gasar Premier ranar 28 ga watan Disamba.

Daraktan wasanni na West Brom Richard Garlick na fatan kawo karshen takaddamar cikin sauri.

Kuma ya ki ya ce komai a kan kokarin da Zoopla kamfanin da kungiyar ke sawa taguwa ke yi na yanke hulda da kungiyar idan Anelka ya ci gaba da buga wasanni.