Ina son Baines ya rattaba kwangila-Martinez

Leighton Baines Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Everton ta kagu da Baines ya rattaba kwangila

Kocin Everton Roberto Martinez ya kagu da dan kwallon Ingila mai tsaron baya Leighton Baines da ya rattaba sabuwar kwangila da kungiyar.

Baines, mai shekaru 29 ana hasashen zai tsawaita kwangilarsa da Toffees da ake ganin za ta kai fan 75,000 a duk mako.

Martinez ya ce "Tsawaita kwangilar Baines abu ne mai mahimmaci da kungiyar, domin an tanadar masa dukkan abubuwan da suka kamata.

"Sauran watanni 18 kwangilarsa ta kare, kuma yakamata mu tsawaita kwangilarsa da mu, sannan yana daga cikin 'yan wasan da muke fatan ya ci gaba da wasa damu.

Baines ya komo Everton kan kudi fan miliyan 6 a watan Agusta 2007, kuma sau biyu tsohon kocin kungiyar David Moyes ya yi kokarin daukar dan wasan zuwa Manchester United.