Tottenham ta doke Swansea 3-1

Swansea Tottenham Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Adebayor ya dawo ganiyarsa tun sanda ya komo wasa

Kwallayen Emmanuel Adebayor guda biyu sun taimakawa Tottenham ta samu nasarar da take matukar bukata kan Swansea City a wasan Premier League.

Emmanuel Adebayor da ya dawo buga wasa karkashin koci Tim Sherwood, shi ne ya zura kwallaye biyu a ragar Swansea da yawancin 'yan wasanta ke jinya.

Adebayor dan kwallon Togo shi ne ya zura kwallon farko a minti na 34 da kwallo ta uku a minti na 70 bayan da dan wasan Swansea Chico Flores ya ci kansu da kansa.

Swansea ta rage yawan kwallayen da aka zura mata ta hannun dan wasanta Wilfried Bony, kuma wannan shi ne wasa na uku a jere da kungiyar ta yi rashin nasara a gasar Premier.

Tottenham ta yi kankankan da Liverpool da maki 43, bayan da ta lashe wasanni biyar daga cikin wasanni shida data buga karkashin sabon kocinta.