Lacina na daf da komawa West Ham

Lacina Traore Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan da ya koma Monako a watan Janairu

Dan wasan Monaco mai zura kwallo a raga Lacina Traore na daf da komawa West Ham a matsayin aro domin buga gasar Premier.

Dan kwallon mai shekaru 23 dan kasar Ivory Coast tuni West Ham ta mika takardar neman izini, da zai samu damar buga wasanni a Ingila.

Sai dai kocin West Ham ya ce duk da sun cimma yarjejeniya yana da wuya dan wasan ya zo ya buga mana wasa a Upton Park.

Monaco na son bada aron dan kwallon da ta sayo daga Anzhi Makhachkala ta Rasha a watan Janairun bana.