CHAN: Nigeria da Mali sun tsallake

Chan 2014
Image caption Najeriya na sa ran lashe kofin karo na farko

Nigeria ta dakile damar Afirka ta kudu na zuwa zagayen gaba a gasar kofin Afirka bayan da ta doke ta da ci 3-1, ta kuma kai zagayen wasan dab da na kusa dana karshe tare da Mali.

Chistantus Ejike shi ne ya zura kwallaye biyu a inda Ifeanyi Ede ya zura kwallo a dukan daga kai sai mai tsaron raga, kuma dukkan kasashen sunyi rashin dan wasa sakamakon jan kati.

Daya wasan rukuni na daya, Mali ta doke Mozambique da ci 2-1, ta kuma samu kaiwa wasan kasashe takwas da za su rage a gasar kuma ja gaba a rukunin da tazar maki daya akan Najeriya.

Najeriya da ke neman lashe wasan don zuwa zagayen gaba ta fara zura kwallo a minti na 21 lokacin da Ejike ya buga kwallo da kafar hagu tun daga tazarar yadi shida ta kuma fada raga.