Za mu iya daukan kofin Premier - Moyes

David Moyes Hakkin mallakar hoto
Image caption Moyes na kiran 'yan wasa su kara kaimi a wasanni

Kocin Manchester United David Mayes har yanzu yana ganin zai rike kambun kofin Premier, duk da tazarar maki 14 da Arsenal mai matsayi na daya a teburin Premier, bayan da Chelsea ta doke ta da ci 3-1.

Samuel Eto'o ne ya zura kwallaye ukun da ya baiwa Chelsea damar lashe wasan, kuma wasa na bakwai kenan da United ta yi rashin nasara.

Moyes, wanda United take matsayi na bakwai a teburin Premier ya ce "har yanzu bamu karaya ba har sai an kare wasanni, fatanmu mu kare a matsayi na daya kuma abinda muke kokarin yi kenan.

Jose Mourinho shi ma bai cire United daga cikin wadanda za su iya daukar kofin Premier ba, amma ya ce sai in har kungiyoyin da suke samansu sun dawo rashin tabuka rawar gani kafin su kare kambunsu.