Everton ta yi kunnen doki da WestBrom

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Diego Lugano ya hana Everton shiga sahun gaba a Premier

Everton ta barar da damar shiga sahun hudun farko a rukunin Premier bayan da kwallon Diego Lugano ta bai wa kocin West Brom Pepe Mel damar samun maki a wasansa na farko a kungiyar.

Kevin Mirallas ne ya ci wa Everton kwallon da za ta iya kai ta matakin buga gasar Zakarun Turai sai dai farkewar da Lugano ya yi da ka, minti 15 kafin tashi daga wasa ta wargaza musu lissafi.

Kocin Everton Roberto Martinez zai ji zafin maki dayan nan ganin yadda 'yan wasansa suka yi ta barar da damarsu kafin rabin lokacin sannan suka sukurkuce baki daya bayan dawowa daga hutu.

Nicolas Anelka na cikin wadanda suka buga wa West Brom kwallo sa'o'i kadan bayan kamfanin Zoopla ya janye alakarsa da kungiyar bisa nunin da Anelka ya yi da hannunsa bayan cin kwallo a West Ham United.

Ana dai danganta alamar ne da goyon bayan akidar Nazi ta kin jinin Yahudawa.