FA ta ki dauka ka karar Vidic kan jan kati

Nemanja Vidic Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan an dakatar da shi wasanni uku nan take

Hukumar kwallon Ingila ta ki amince wa da daukaka karar da kaftin din Manchester United Nemanja Vidic ya shigar a kan jan katin da aka bashi a karawar da suka yi da Chelsea.

Nan ta ke Jan katin da aka bashi na dakatar da shi wasanni uku ya fara aiki, ba zai buga karawar da kungiyar za ta yi da Sunderland a ranar Laraba a kofin Capital One wasan kusa da na karshe ba.

Vidic, mai shekaru 32 an bashi jan kati kai tsaye a kyetar da ya yiwa dan kwallon Chelsea Eden Hazard a wasan da aka doke su da ci 3-1 a Stamford Bridge ranar Lahadi.

Ba zai buga wasan da United za ta karbi bakuncin Cardiff da kuma karawar da za suyi da Stoke ba.

Karo na shida ana baiwa Nemanja Vidic jan kati tun lokacin da ya dawo wasa a Manchester United a shekarar 2006, guda uku a karawa da Liverpool, biyu a wasa da Chelsea da kuma daya a kofin zakarun Tuari a wasa da Otelul Galati.

Wata hukuma ce mai zaman kanta taki karbar daukaka karar da ya shigar ranar Talata.