Zuma ya kare Bafana Bafana

Jacob Zuma Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasar ta kasa kaiwa wasan daf da na kusa da karshe

Shugaba Jacob Zuma ya kare 'yan kwallon kafar kasar bayan da suka kasa kaiwa wasan daf da na kusa da karshe a gasar kofin Afirka ta 'yan kwallon gida.

Shugaban hukumar wasannin kasar Fikile Mbalula ya kira 'yan wasan da ce wa basu da amfani kuma taron tsintsiya ba shara.

Zuma ya sanar a wata tashar radiyo dake Afirka ta kudu ce wa "Duk da cewa an doke mu, ba komai tunda wasu kasashen su ma an doke su.

"Wasu na kiran da a wargaza 'yan wasan. Suna samun ci gaba a wasanninsu kuma suna bukatar goyon bayan mu."

Najeriya ce dai ta doke Afirka ta kudu da ci 3-1 a karawar da suka yi a Cape Town.