Wawrinka ya yi waje da Djokovic a Australia

Stanislas Wawrinka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan ya yi murnar lashe wasan da ya yi

Stanislas Wawrinka ya yi waje da Novak Djokovic a kwallon Tennis da ake fafatawa a Australia a wasan daf da na kusa da karshe, ya kuma kawo karshen kudurin Djokovic na daga kofin a karo na hudu a jere.

Dan wasan Switzerland na takwas a duniya, Stanislas Wawrinka ya lashe wasan ne da jibin goshi inda wasan ya kai har turmi biyar, to saidai masu iya magana na cewa "da kyar na sha ya fi da kyar aka kama ni."

A wasan kusa da na karshe, zai kara ne da Tomas Berdych.

Rashin nasarar da Djokovic ya yi ita ce ta farko karkashin sabon kocinsa Boris Becker, kuma karshen lashe wasanni 28 a jere a gasa daban-daban, sannan karshen lashe wasanni 25 cikin shekaru uku a Melbourne.

Wawrinka mai shekaru 28 ya ce "Zakakurin Zakara ne, ba a doke shi cikin sauki, hakika nayi murna matuka."