'Rashin farin jinin gasar Commonwealth'

Gold Coast Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasannin yana lashe kudade da dama

Hukumar gudanar da wasannin Common wealth ta damu matuka da rashin nuna sha'awar daukar bakuncin gasar daga mambobin kasashe a wasannin masu zuwa na gaba.

A yanzu babu wata mamba daga kasashen da ta nuna sha'awar karbar bakuncin wasannin 2022 da a watan Maris za a rufe karbar takardar mika bukatar daukar nauyin gasar.

Kimanin mambobin kasashen 71 sun amince cewar zashin gogayyar yunkurin karbar bakuncin gasar zai raunata gudanar da wasannin a nan gaba.

Za a gudanar da wasannin karo na 20 a Glasgow ranar 23 ga watan Yuni, da kuma birnin Gold Coast na Australiya da zai karbi bakuncin wasannin 2018.

Matsalar kudi ce ke kawo tsaikon karbar bakuncin gasar, domin wasannin Glasgow an kiyasata zai ci kudi fan miliyan 500.